<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Sai ku tashi dai mutane duk
 Ku ji labarin mu
 La...barin mayaki na Mai Ceto
 Idan za ka ci nasara
 Cikin yaƙin nan sosai
 Sai ka nuna bangaskiya da aminci.

[V2]
 KORUS
 Mayaƙi....na Yesu Kristi
 Sai ka nuna halin kirki
 Sai ka dogara gareshi
 Ubangiji za shi bada nasara.

[V3]
 2) Duk maganar Ubangijinmu
 A buɗe ta ke kuwa
 Bari dai mu yi biyayya ba shakka
 Ko Shaiɗan ya jarrabce mu
 Ga mu nan da takobi
 Sai mu ci gaba da ƙarfin zuciya.
 Korus

[V4]
 3) A cikin yaƙin nan gaban mu
 Mu yi tsayayya kuwa
 Shaiɗan dai zai guje mamu nan da nan
 Mu taimaki ƴanuwanmu
 Mu yi shaida fa
 Har ya zo ya kai mu gidan sama a can.
 Korus</lyrics>
<title>Sai Ku Tashi Dai Mutane Duk LW513</title>
<hymn_number>513</hymn_number>
<author>Black, James Milton (1856-1938)</author>
</song>